in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta ce za ta rika bada visa bayan isa kasar ga 'yan Afrika daga wata mai zuwa
2018-10-27 16:24:29 cri
Gwamnatin kasar Habasha za ta fara bada visa ga dukkan 'yan Afrika bayan sun isa kasar, daga ranar 9 ga watan Nuwamba.

Shugaban ma'aikatan firaministan kasar Fitsum Arega, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, tsarin bada visa bayan isa kasar ga 'yan Afrika masu ziyara, ya yi daidai da burin Firaministan kasar Abiy Ahmed na tabbatar da dunkulewar nahiyar.

Habasha na fatan shirin zai taimaka wajen saukaka dunkulewar tattalin arzikin nahiyar Afrika ta hanyar kara ingantawa da bunkasa harkokin yawon bude ido.

Kasar ta gabashin Afrika da ta kasance mazauni ga hedkwatar Tarayyar Afrika AU, na fatan yunkurin zai taimakawa shirin AU na tabbatar da zirga-zirga jama'a ba tare da shinge ba. AU ta bukaci dukkan kasashen Afrika su rika bada bisa bayan isa kasar ya zuwa shekarar 2023. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China