Zirga zirgar jirgin saman na Habasha zuwa babban birnin kasar ta Rasha shi ya kawo matsayin zirga zirgar jirgin zuwa dukkannin kasashe 5 na kungiyar BRICS.
Da yake bayyana matsayin fara zirga zirgar jirgin saman kai tsaye daga Afrika zuwa Rasha, shugaban kamfanin jirgin saman na Ethiopian Airlines, Tewolde GebreMariam, ya ce zirga zirgar da jirgin zai fara gudanarwa wanda zai sada Afrika da Rasha, wata muhimmiyar dama ce da za ta kara bunkasa dangantaka tsakanin shiyyoyin biyu.(Ahmad Fagam)