in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin zai kafa reshe a kasar Habasha domin bunkasa ayyukansa
2018-10-29 09:55:33 cri
Sakamakon bunkasuwa da ake samu a kasar Habasha a halin yanzu, kamfanin gine gine na (CCCC) na kasar Sin ya kammala shirye shirye domin bude ofishin shiyya a kasar ta gabashin Afrika, in ji wani jami'in kamfanin.

A yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, mataimakin janar manajan kamfanin na CCCC mai kula da shiyyar gabashin Afrika Wei Qiangyu, ya ce an shirya kafa reshen kamfanin na shiyyar Afrika ne a Habasha, sakamakon girman ayyukan da kamfanin ke gudanarwa a kasar da ma sauran kasashe dake shiyyar kamar Kenya da Uganda wadanda ke karuwa cikin sauri.

"Sabon ofishin shiyyar za'a kafa shi ne a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha wanda zai kunshi cibiyoyin fasaha da kirkire kirkire, za'a zuba kayayyakin gwaje gwaje na zamani, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukanmu bisa kwarewa kuma a kan lokaci, ayyuka masu yawa muke gudanarwa da suka hada da layin dogo, filin jiragen sama, da gina titunan mota wadanda muke gudanarwa a Habasha har ma da sauran wurare," in ji Wei. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China