Adadin na kayayyaki ne da aka saya a ranar Asabar kadai, wanda ya karu a kan na bara da kaso 29.4.
Ranar Gwagware ta 11 ga watan Nuwamba, ta zama wata rana ta sayayya a yanar gizo ne tun bayan da kamfanin Alibaba ya fara bada garabasa a shekarar 2009.
Garabasar da kamfanin Alibaba ya yi a bana, ya kai yuan biliyan 168.3 kwatankwacin dala biliyan 25.4, wanda ya karu a kan yuan biliyan 120 na bara. Shi ma kamfanin JD.com da ya fara garabasa a farkon wannan watan, ya ce an yi sayayyar yuan biliyan 127.1
A cewar mataimakin daraktan hukumar SPB, ranar kalubale ce ga bangaren masu samar da kayayyaki ta fuskar ingancin hidima da yawan kayayyaki da aka saya.
Hukumar na sa ran kunshin kayayakin da za a kai wa mutanen da suka yi sayayya zai kai biliyan 1.5 tsakanin ranakun 11 da 16 ga watan nan, wanda ya karu da kaso 35 a kan na bara. Abun da ke nuna cewa, adadin kayayyakin da a kan aike da su kowace rana zai ninka har sau 3 a kan yadda aka saba. (Fa'iza Mustapha)