Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci domin samun ingantacciyar ci gaba, tare da yin kira da a himmantu wajen ganin dorewa tsarin kasuwanni.
A wani umarni da ya bayar jiya ga taron sa ido kan harkokin kasuwanci, Li Keqiang ya ce an samu ingantuwar yanayin kasuwanci cikin shekaru kalilan da suka shude biyo bayan sauye-sauye da aka yi a bangaren.
Ya ce samun kyakkyawan yanayin kasuwanci na da muhimmanci ga bunkasar tsarin tattalin arziki na zamani da samun ingantacciyar ci gaba.
Firaministan ya ce ya kamata kasar Sin ta ci gaba da sauya harkokin gudanarwa da bada iko ga matakai na kasa da kuma inganta ayyuka.
Li Keqiang ya ce dole ne a samar da sabbin hanyoyin sanya ido kan harkokin kasuwanci, sannan a kara kaimi wajen ganin dorewar tsarin kasuwanci da takara mai adalci. (Fa'iza Mustapha)