in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta guji daukar matakan bada kariya ga harkokin kasuwanci
2018-01-23 16:07:46 cri
A jiya Litinin, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da sanya haraji kan manyan injunan wanke tufafi, harajin da za a aiwatar cikin shekaru uku masu zuwa, da kuma batura na farantan dake samar da wutar lantarki bisa hasken rana cikin nan da shekaru hudu masu zuwa, wadanda Amurka take shigowa da su daga kasashen waje.

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta nuna matukar rashin jin dadinta game da wannan mataki da Amurka ta dauka, inda wani babban jami'in ma'aikatar mai suna Wang Hejun ya bayyana fatansa na cewa, Amurka za ta guji daukar matakan bada kariya ga harkokin kasuwanci, da mutunta ka'idojin gudanar kasuwanci na bangarori daban-daban.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China