Abdouraman Bary, jami'in sashen kula da sinadarai, shara da inganci iskar da ake shaka na MDD mai kula da shiyyar Afrika, ya shedawa taron kolin kasashen Afrika a Nairobi cewa, kasashen suna fama da matsalar karuwar tarin bola sakamakon karuwar da ake samu na amfani da kayayyakin latironi a nahiyar.
Bary yace, samar da managartan tsare tsaren da zasu tabbatar da inganta sarrafa shara zai taimakawa nahiyar wajen shawo kan matsalar karuwar tarin bola, ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ranar kula da shara ta kasa da kasa.
Ya ce tsare tsaren za su taimaka wajen kara kaimi da gwarin gwiwa a fannin sarrafa bola domin rage yawan tarkacen latironi da ake tarawa.
Jami'in ya bukaci a samar da wasu dokokin hana shigo da kayayyakin latironi da wa'adin amfani da su ya kusa karewa sakamakon matsalar da suke haifawar nahiyar na kara dattin bola. (Ahmad Fagam)