in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: Sudan ta kudu tana fuskantar kalubalen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma
2018-09-19 10:34:42 cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan tabbatar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya bayyana a jiya Talata cewa, gwamnati da bangaren 'yan adawar kasar Sudan ta kudu suna fuskantar kalubale wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da suka cimma.

Da yake yiwa zaman kwamitin sulhun majalisar karin haske, jami'in ya ce yarjejeniyar da shugaban kasa Salva Kiir da jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar suka sanyawa hannu a ranar Larabar da ta gabata, wani muhimmin ci gaba ne, duba da yadda ta samar da taswirar samar da zaman lafiya ta hanyar aiwatar da gyare-gyare, farfado da harkokin siyasar kasar, inganta matakan tsaro, jin dadin jama'a da raya tattalin arziki da kuma sasanta 'yan kasar.

Sai dai kuma jami'in na MDD ya yi gargadin cewa, duk da kasancewar abubuwan da ake bukata na samun nasarar hakan, akwai wasu muhimman tambayoyi gami da damuwa da ake nunawa dangane da aniyar bangarorin na mutunta yarjejeniyar, baya ga wasu fannoni da dama na zahiri dake da nasaba da aiwatar da yarjejeniyar da har yanzu ke bukatar tantancewa.

Ya ce, matakin farko da bangarorin ya dace su dauka, shi ne dakatar da tashin hankali ba tare da bata lokaci ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China