in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kwashe 'yan gudun hijrah masu rauni 135 daga Libya zuwa Niger
2018-10-19 10:07:00 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta kwashe 'yan gudun hijira da masu neman mafaka dake da rauni guda 135 daga Libya zuwa Niger.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta yi nasarar kwashe mutanen daga Libya ne ranar Talata da dare, duk da yadda ake tsaka da fama da rashin tsaro a birnin Tripoli.

Shugaban ofishin hukumar a Libya Roberto Mignone, ya bayyana kwashe mutanen a matsayin ceton rayukan 'yan gudun hijirar da suka makale a Libya.

Ya ce 'yan gudun hijirar da bakin haure dake cibiyoyin da ake tsare da su, na cikin mummunan yanayi, sannan suna fuskantar barazanar sayarwa ga masu fasa kauri da masu safarar bil adama.

Haka zalika a ranar, wasu 'yan gudun hijira 85 da suka hada da 'yan kasar Syria da Sudan da Eritrea, sun bar Tripoli cikin jirage biyu zuwa birnin Timisoara dake yammacin Romania, bisa taimakon hukumar kula da kaura ta duniya, inda za a kai su Norway bayan makonni 2.

Tun daga watan Disamban 2017, hukumar UNHCR ta yi nasarar kwashe 'yan gudun hijira 1,997 daga Libya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China