in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'ajiyar abincin makarantu ta Tunisia za ta taimaka wajen samar da sinadaran gina jikin yara
2018-10-22 11:17:10 cri
Ministan ilimi na Tunisia, Hatem Ben Salem, ya ce samar da ma'ajiyar abinci na makarantu, zai taimaka tare da bunkasa shirin ciyarwa na makarantun.

Hatem Ben Salem, ya bayyana haka ne yayin bude taron Dandalin kasa da kasa karo na 20, kan abinci mai gina jikin yara, wanda aka yi a birnin Tunis, da ya samu halartar Firaministan Tunisia Youssef Chahed da wasu mahalarta 300 daga kasashe 50.

Ministan ya ce babban abun da suka sa a gaba shi ne, cimma munafar bai daya ta kasashen Larabawa ta kula da abubuwa masu gina jikin yara.

Baya ga gudunmawa daga gwamnati, bangarori masu zaman kansu da kungiyoyin al'umma, su ma za su taimaka wajen samar da kudaden samar da abincin.

Firaministan Tunisia, Youssef Chahed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yayin da adadin masu shiga makaranta ke tunkarar kaso 100 bisa 100, an shiga matakin samun sauyi daga hakkin samun ilimi zuwa samun ingantaccen ilimi.

Ita kuwa Daraktar zartaswar dandalin tattauna batutuwan abinci mai gina jikin yara na duniya, Arlene Mitchell, cewa ta yi, manufar taron ita ce, tattauna batutuwan da suka shafi ababen gina jikin yara a fadin duniya, da nufin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe, domin karfafa musu gwiwar samarwa da inganta shirin ciyarwa a makarantu, wanda ke taimakawa ga samun ci gaba mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China