in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da rashin tsaro a kudancin Libya
2018-10-20 16:37:34 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Libya UNSMIL, ya yi tir da rashin tsaro da ake fama da shi a kudancin Libya.

Shirin ya yi Allah wadai da tabarbarewar yanayin tsaro a kudancin Libya, inda ya yi kira ga hukumomin kasar su daukin matakan da suka dace game da rashin doka da oda a yankin.

Shirin ya kuma yi kira da masu ruwa da tsaki na yankin arewacin Afrika, su mara baya ga hukumomin kasar wajen magance yanayin bisa girmama 'yancin cin ganshin kai da kasar ke da shi.

Shirin ya kuma bayyana damuwa game da karuwar laifuffuka da sace-sacen mutane da lalata kayayyakin samar da ruwa na gwamnati.

Ita ma Gwamnatin kasar da MDD ta amince da ita, ta yi kira da a hada hannu wajen adawa da dakarun haya na kasashen waje dake kudancin kasar.

A cewar wata kafar yada labarai ta kasar, rikici ya barke tsakanin jami'an tsaron kasar da dakarun haya daga kasar Chadi a ranar Lahadi da Litinin da suka gabata, a wani wuri dake kusa da birnin Um Ai-Araneb dake yankin kudancin kasar, wanda ke da nisan kilomita 950 daga kudancin birnin Tripoli, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 4. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China