in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma sabuwar yarjejeniyar kwashe 'yan tawayen Syria daga wajen Homs
2018-05-02 09:38:15 cri
A jiya Talata ne aka cimma wata sabuwar yarjejeniya kan yadda za a kwashe 'yan tawaye da iyalansu daga wajen arewacin lardin Homs dake tsakiyar kasar Syria. Wannan shi ne mataki na baya-bayan da aka cimma tsakanin gwamnati da 'yan tawayen game da wannan batu.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria (SANA) ya sanar da cewa, sabuwar yarjejeniyar za ta kai ga kwashe 'yan tawaye da iyalan nasu daga wuraren da suke rike da su a wajen arewacin Homs zuwa yankunan dake arewacin birnin Jarablus da arewa maso yammacin lardin Idlib. Ana dai sa ran kammala kwashe 'yan tawayen cikin kwanakin uku, kana 'yan tawayen da ba sa son barin yankunan, za su sasanta da gwamnati kana su ci gaba da zama a birnin na Homs.

Sai dai kuma, wajibi ne 'yan tawayen su mika makamansu masu hadari cikin kwanaki biyu bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, a matsayin wani sharadi na yarjejeniyar kwashe su. Aiwatar da wannan yarjejeniya na nufin cewa, za a kawar da 'yan tawaye baki daya daga lardin na Homs. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China