in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya tattauna da Rouhani kan batun Syria
2018-04-16 11:00:06 cri

Jiya Lahadi 15 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tattauna da takwaransa na kasar Iran Hassan Rouhani kan batun kasar Syria ta wayar tarho, inda shugabannin biyu suka bayyana cewa, matakin soja da Amurka da kawancenta suka dauka a kasar Syria ya sabawa dokar kasa da kasa, wanda zai kawo illa kwarai ga kokarin da ake yi na warware rikicin kasar Syria a siyasance.

Shafin yanar gizo ta Intanet na fadar shugaban Rasha ya nuna cewa, shugabannin Rasha da Iran sun yi musanyar ra'ayi kan halin da Syria ke ciki bayan matakin sojan da Amurka da kawancenta suka dauka kan kasar. Inda Putin ya jaddada cewa, halin da duniya ke ciki zai girgiza idan irin wannan mataki mai sabawa tsarin mulkin MDD ya sake aukuwa a nan gaba.

An ba da labari cewa, kwanan baya an yi kirari cewa, akwai makamai masu guba a yankin gabashin Ghouta dake karkarar birnin Damascus. Sojojin Amurka da Birtaniya da Faransa sun kaddamar da farmaki kan gine-ginen dakarun sojan kasar ta Syria a daren ranar 13 ga wata bisa agogon gabashin Amurka. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China