in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman yaki na Iraqi ya kai hari kan sansanin IS dake kasar Sham
2018-08-17 10:34:43 cri

Rundunar sojojin kasar Iraqi ta bayyana a jiya Alhamis 16 ga wata cewa, wani jirgin saman yaki na kasar ya kai hari kan wani sansanin IS dake kasar Sham, lamarin da ya haddasa rasuwar wasu 'yan ta'adda da dama.

A cikin wata gajeriyar sanarwar ta hedkwatar rundunar aikin hadin gwiwa ta Iraqi ta fitar, an ce bisa hakikanin sakon da aka bayar, jiragen saman yaki na Iraqi samfuri F-16 sun kai hari ta sama, inda suka cimma nasarar murkushe wata helkwatar rundunar, suka kuma hallaka wasu 'yan ta'adda da suka shirya kai hari kasar ta Iraqi a kwanan baya.

Amma sanarwar ba ta fayyace hakikanin lokaci da wurin da lamarin ya wakana ba.

An ce, tun daga watan Disamba na shekarar bara, firaministan Iraqi Haider al-Abadi, ya sanar da cimma nasarar dakile IS, amma a wasu yankunan hamada dake kan iyakar kasar ta Iraqi da ta Sham, 'yan ta'adda na cin karen su ba babbaka a kokarinsu na haifar da tashin hankali. Ya zuwa wannan shekara dai, sojin Iraqi sun kai hare hare ta sama sau da dama kan sansanin kungiyar IS dake cikin harabar kasar ta Sham. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China