Sanarwar da kakakin ma'aikatar Khaled Megahed ya fitar, ta ce rahoton baya-bayan nan na nuni da cewa, mahajjata biyu sun mutu sanadiyyar matsananciyar ciwon zuciya da na numfashi.
Ya kara da cewa, hukumomin kasar na aiki da takwarorinsu na Saudiyya domin samun takardar shaidar mutuwar mahajjatan.
Mace-mace sanadiyyar zafi da gajiya da sauran wasu abubuwa indallahi, abu ne da aka saba gani yayin aikin hajji a Saudiyya.
Sama da mahajjata 84,000 'yan kasar Masar ne suka sauke farali bana, inda jimilar al'ummar duniya da suka yi aikin hajjin ya kai miliyan 2.4.
A bara, sama da mahajjatan Masar 80 ne suka mutu daga cikin mahajjata 70,000. (Fa'iza Mustapha)