Shugaba al-Sisi na bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk da shugaban gwamnatin Austria, Sebastia Kurz dake ziyara a Masar.
Sanarwar da fadar shugaban Masar ta fitar, ta ruwaito shugaban ya kuma bayyana kokarin kasarsa na yaki da kwararar bakin haure da kare iyakokinta na kasa da na ruwa, yayin da ake tsaka da fama da rashin tsaro a kasashen dake makwabtaka da ita.
Sanarwar ta ce Abdel-Fattah al-Sisi da bakin nasa, sun kuma tattauna kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, musammam Libya da Syria, inda ta ce dukkansu sun amince cewa maslahar siyasa ce za ta kawo karshen rikicin da kwararar bakin haure.
A baya, Masar ta kasance inda bakin haure ke bi don tsallakawa zuwa Libya akan hanyarsu ta zuwa Turai ta tekun Bahar Rum. (Fa'iza Mustapha)