in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta yi maraba da yarjejeniyar Jeddah ta wanzar da zaman lafiya tsakanin Habasha da Eritrea
2018-09-17 19:16:15 cri
A yau Litinin ne mahukuntan kasar Masar suka bayyana farin cikin su, bisa sanya hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ta birnin Jedda na kasar Saudi Arabia, yarjejeniyar da ta tanaji daukar matakan sulhu tsakanin kasashen Habasha da Eritrea.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar, ta ce yarjejeniyar na da matukar muhimmanci ga yankin kahon Afirka. Kaza lika za ta tallafa wajen kawo karshen rashin jituwa da kasashen biyu 'yan uwan juna suka shafe tsawon lokaci suna fama da shi. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China