Ya ce, batun yaki da ayyukan ta'addanci na kan gaba cikin ajandar ganawar, sauran sun hada da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da kuma batutuwa da ke shafarsu.
Kasashen uku dai su ne ke kokarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria, kuma tun a shekarar 2016 suke kokarin shiga tsakani a shirin tabbatar da zaman lafiya game da rikicin kasar ta Syria.
A ranar Jumma'a mai zuwa ne ake sa ran shugaba Hassan Rouhani na Iran da takwarorinsa na kasashen Rasha Vladimir Putin da na Turkiya Recep Tayyip Erdogan za su gana a birnin Tehran na kasar Iran. (Ibrahim)