in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Netanyahu ya sha alwashin cigaba da kai hare hare ta sama a Syria
2018-09-26 11:11:12 cri

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a jiya Talata cewa dakarun tsaron Isra'ila (IDF) za su cigaba da kaddamar da hare hare ta sama kan dakarun Iran dake Syria, duk da kasancewar Rasha ta tura na'urorin S-300 masu kare hare haren makamai masu linzami.

"Za mu cigaba da yin aiki domin hana dakarun tsaron Iran kafa sansani a Syria kuma za mu cigaba da aikin tabbatar da tsaro tsakanin dakarun tsaron IDF da sojojin Rasha," Netanyahu ya bayyanawa manema labarai jim kadan kafin ya tashi zuwa birnin New York don halartar babban taron MDD.

Shugaban na Isra'ila ya ce, Isra'ila "tana matukar samun nasarori" a cikin shekaru ukun da suka gabata wajen hana dakarun sojojin Iran samun gindin zama a Syria da kuma hana su yunkurin tura makamai ga mayakan Hezbollah dake kasar Lebanon. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China