in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha na duba yiwuwar bunkasa fitar da ridi zuwa kasar Sin
2018-10-24 10:20:01 cri
Manoma da masu fitar da ridi na Habasha, na sha'awar kara bunkasa shigar da hajarsu kasuwar kasar Sin, yayin da ake tsaka da samun karuwar bukatar ridin daga Sinawa.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Haile Berhe, shugaban kungiyar masu sarrafawa da fitar nau'ikan wake da kayan yaji da kuma amfanin gona dake samar da mai ta kasar, ya ce kayayyakin da a yanzu kasar ke fitar zuwa kasar Sin, sun kai kaso 70 na jimilar abun da kasar ke fitarwa zuwa kasuwar duniya.

Ya ce kasuwar ridi ta kasar Sin ta zama babbar kasuwa ga masu noma da fitar da kayayyaki na Habasha, inda ya ce ana kuma samun karuwar bukatar ridin kasar a tsakanin Sinawa masu saye.

A cewarsa, baje kolin kayayyakin da ake shiga da fitar da su daga kasar Sin na farko da za a yi daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba a Shanghai na kasar Sin, zai taimakawa 'yan kasuwar Habasha dake fitar da kayayyaki rike kabunsu a kasuwar ridi ta kasar Sin, al'amarin da zai taimaka musu kara shiga kasuwanni.

Ma'aikatar kula da cinikayya ta Habasha, ta ce yayin da ake cikin shekarar kudi ta 2017/2018 da ta kare a ranar 8 ga watan Yulin, kasar ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dala miliyan 245 zuwa kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China