Cikin wani sakon taya murna ta shafin tweeter, ofishin UNSMIL ya taya sabbin wadanda aka nada din karkashin gwamnatin hadin kan kasa ta GNA murna, tare da fatan samun cikakken goyon bayan MDDr.
Kaza lika ofishin ya ce zai ci gaba da tallafawa ministocin, wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro a birnin Tripoli, da fadada matakan sauya tsarin tattalin arzikin kasar, da kuma samar da daidaito a tsakanin hukumomin kasar. (Saminu Alhassan)