Biyo bayan ganawar da ya yi da shugaban hukumar AU Musa Faki Mahamat dake ziyara a Algiers, Messahel ya shaidawa manema labarai cewa, taron zai gudana ne a ranar 9 ga watan Afrilu, inda ya ce tuni ya samu sahalewar kwamitin sulhu na AU a watan Satumban 2014, domin inganta hadin kai wajen yaki da ta'addanci a tsakanin kasashen Afrika.
Abdelkader Messahel ya kara da cewa, taron na da matukar muhimmanci la'akari da yanayin da ake ciki a yanzu, domin zai bada dama ta musayar ra'ayi kan dokokin yaki da ta'addanci a kasashe mambobin AU da kuma cimma matsaya daya a tsakaninsu a wannan bangare.
Har ila yau, ya ce taron na da nufin bayyana rawar da hukumomin nahiyar Afrika ke takawa a fannonin yaki da ta'addanci da halasta kudin haram da fasa kauri da sauran laifuka. (Fa'iza Mustapha)