in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kaso 70 bisa dari na ridin da ake fitarwa daga Habasha na shiga kasuwannin Sin
2018-10-23 20:36:47 cri
Shugaban kungiyar masu fitar da ridi da dangogin sa na kasar Habasha Haile Berhe, ya ce kaso kusan 70 bisa dari, na ridin da ake fitarwa daga Habasha na shiga kasuwannin kasar Sin ne.

Haile Berhe, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan ne a Talatar nan, yana mai cewa kasuwar ridi ta Sin, ta zamo jigo ga hada hadar cinikayyar sa tsakanin 'yan kasuwar Habasha, a daidai gabar da 'yan kasuwar Sin masaya ke dada nuna bukatar sa.

Ridi da 'ya'yan gahawa, na cikin hajojin dake kan gaba a fagen samarwa Habasha kudaden shiga, matakin da kuma ya zama kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasar baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China