in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar likitocin Najeriya ta yi Allah wadai da kaddamar da hari kan ma'aikatan lafiya
2018-10-19 10:00:32 cri
A jiya Alhamis kungiyar likitoci ta Najeriya ta yi Allah wadai da kisa na baya bayan nan da kungiyar Boko Haram ta yiwa ma'aikaciyar lafiya ta kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Obitade Obimakinde, kakakin kungiyar ma'aikatan lafiyar Najeriya, ya fada cikin wata sanarwa cewa, kungiyar ta bayyana kashe ma'aikatan lafiyar a matsayin abin tada hankali wanda ka iya yin illa ga makomar rayuwar bil adama.

Ma'aikaciyar lafiyar wacce mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da ita tun a watan Maris na wannan shekara, tare da wasu ma'aikatan na ICRC biyu.

Ma'aikatan agajin 3 suna aiki ne a wani asibiti dake samun tallafin kungiyar agajin ta Red Cross a sansanin 'yan gudun hijira dake wani kauye a jahar Borno, a baya, garin ya taba zama daya daga cikin yankunan da mayakan Boko Haram suke rike da shi.

Ma'aikaciyar ta ICRC ita ce ma'aikaciyar agaji ta biyu da mayakan suka hallaka bayan sun yi garkuwa da su cikin wata guda.

Da take bayyana farin cikinta bisa irin kokarin da gwamnati ke yi, kungiyar likitocin ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a, musamman wadanda ke gudanar da ayyukan jin kai a fadin kasar.

Kakakin kungiyar ya kara da cewa, samar da ingantattun matakan tsaro zai taimaka wajen magance matsalolin ayyukan ta'addanci da yin garkuwa da mutane da mayakan Boko Haram ke kaddamarwa a fadin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China