in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya sanar da bude babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao
2018-10-23 16:07:57 cri
Yau Talata da safe, aka yi bikin kaddamar da babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao a birnin Zhuhai na lardin Guangdong. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wannan biki, inda ya kuma sanar da bude babbar gadar a hukumance, kana ya kalli gadar.

Xi Jinping ya jaddada cewa, gina babbar gadar dake hada Hongkong da birnin Zhuhai da yankin Macao ta kafa sabuwar bajinta a wasu fannoni a duniya, wadda ta bayyana tunanin yin kokarin gina hanyoyi a kan duwatsu da gina gada a kan ruwa, kana ta shaida karfin kasar Sin da karfin yin kirkire-kirkire da kanta da kuma yin kokarin kasancewa a matsayi na kan gaba a duniya. Wannan gada ta shaida tunanin cimma buri da hada kai da yin imani da kanta da samun farfadowa. Bayan da aka bude gadar, an kara kiyaye tutanin yin imani kan hanyoyi da ka'idoji da tsari da al'adu na tsarin gurguzu na musamman mai alamar kasar Sin, wannan ya shaida cewa, ana kokarin gudanar da ayyuka don raya tsarin gurguzu a sabon zamani.

Za a fara yin zirga-zirgar motoci a gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao a ranar 24 ga wannan wata. Ana shirin yin amfani da gadar har na tsawon shekaru 120, kana tsawonta ya kai kimanin kilomita 55, wadda lardin Guangdong da yankin Hong Kong da yankin Macao suka yi hadin gwiwar ginawa a karo na farko, kana za a sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannonin yin jigila da tattalin arziki da cinikayya da yin kirkire-kirkire kan kimiyya da fasaha da sauransu, ta haka za a raya yankin Guangdong da Hong Kong da Macao a nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China