Xi Jinping ya kai ziyara yankin fasahohin zamani na Hengqin dake birnin Zhuhai da farko, wannan ne karo na 4 da Xi Jinping ya kai ziyara a wurin a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Xi Jinping ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, ana samun babban canji a yankin Hengqin. Ya kamata mu tuna da burinmu na farko, da kara yin kirkire-kirkire, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki a fannoni daban daban a yankin Macau.
Bayan da ya tashi daga yankin Hengqin, sai shugaba Xi Jinping ya kai ziyara a kamfanin GREE, wanda ya samar da na'urorin sanyaya daki, da na'urorin zamani, da kuma na'urorin amfanin yau da kullum, kana an sayar da su a kasashe da yankuna fiye da 160 a duniya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kamfanonin Sin su ci gaba da kokarin yin kirekire-kirkire da kansu, da inganta karfinsu a wannan fanni. (Zainab)