in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya murnar budewar taron dandali na Xiangshan
2018-10-25 13:10:12 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya murnar bude taron dandali na Xiangshan a birnin Beijing, a yau Alhamis.

Cikin sakonsa, shugaban ya ce, a wannan zamanin da ake ciki jama'ar duniya suna rungumar zaman lafiya, ci gaba, hadin gwiwa, da samar da moriya ga juna, haka kuma ana kokarin daidaita tsare-tsaren kula da al'amuran duniya. A wannan lokaci ana ci gaba da fuskantar wasu kalubaloli a fannin tsaro, sai dai kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta hadin gwiwa, da kara bude kofa ga kasashen waje, don tabbatar da gina wata al'ummar duniya mai kyakkyawar makoma irin ta bai daya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China