in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya karfafawa 'yan kasuwa gwiwar kara yin kirkire-kirkire da kere-kere
2018-10-22 10:54:15 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa kamfanoni masu zaman kansu gwiwar yin ammana ga samun ci gaba da gudanar da harkokinsu bisa kan-kan da kai, domin bunkasa kasuwancinsu.

Shugaban Xi ya bayyana haka ne cikin wata wasikar da ya rubuta dangane da karrama wasu 'yan kasuwa da aka yi, wadanda suka bada gudunmawa ga aikin yaki da talauci

Cikin wasikar, shugaban ya yaba kwarai da jajarcewar 'yan kasuwar ga shirin yaki da talauci.

Ya ce ya yi murna da ganin karuwar adadin 'yan kasuwa dake sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na taimakawa al'umma, inda suke dukufa ga aikin yaki da talauci da taimakawa marasa galihu.

Sama da 'yan kasuwa 60,000 ne suka shiga gangamin yaki da talauci da aka yi wa lakabi da "'yan kasuwa 10,000 masu taimakawa kauyuka 10,000" tun bayan kaddamar da shi a watan Oktoban 2015, inda aka karrama 100 daga cikinsu a farkon watan nan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China