in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin kafa talabijin mai tauraron dan adam zai amfanawa al'ummomi 300 a Ghana
2018-09-27 09:56:23 cri
Bisa ga taimakon gwamnatin kasar Sin, kimanin al'ummar kasar Ghana 300 dake zaune a yankunan karkara ne za su ci moriyar aikin samar da tashar talabijin ta zamani mai tauraron dan adam wanda aka kaddamar a ranar Laraba.

Jakadan kasar Sin a Ghana Wang Shiting, da ministar sadarwar kasar Ghana Ursula Owusu-Ekuful su ne suka jagoranci kaddamar da aikin a Dansoman, a yankin Accra, babban birnin kasar ta Ghana.

Aikin wani bangare ne na gwamnatin kasar Sin na samar da tashoshin talabijin mai tauraron dan adam dubu 10 a nahiyar Afrika.

"Aikin wani yunkuri ne na tallafawa mazauna yankunan karkara don samun damar mallakar talabijin don bibiyar abubuwan dake faruwa a kasashensu da duniya baki daya da kuma kallon shirye shiryen da za su kara ilmantar da al'umma da inganta jin dadin rayuwarsu," in ji Wang.

Jakadan ya ce, aikin zai kara samar da damammaki ga matasa wadanda za'a ba su horo game da yadda ake tafiyar da ayyukan na'urorin a yankunansu, kuma aikin zai samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 1 ga 'yan kasar Ghana.

Magidanta dubu 6 da al'ummomi 900 ne ake sa ran za su ci gajiyar shirin.

Owusu-Ekuful ta ce aikin zai bada taimako har guda biyu na samar da haske ga al'ummomin yankuna da kuma ba su damar amfani da talabijin na zamani mai tauraron dan adam. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China