in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da masu aikin sa kai 5,000 za su ba da tallafi yayin bikin baje kolin kayan da ake shigowa da su Sin
2018-09-29 16:50:16 cri

Sama da masu aikin sa kai 5,000 ne za su ba da tallafi, yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su Sin na bana ko kuma CIIE a takaice, bikin da zai kasance irinsa na farko da kasar za ta karbi bakunci, a cewar kwamitin matasan JKS na birnin Shanghai.

Mafi yawan masu aikin sa kan dai dalibai ne daga jami'oin Sin, da kuma sauran dalibai na manyan makarantun kasar. Ana kuma fatan za su ba da tallafi ga masu halartar baje kolin da harsunan turancin Ingilishi, da Japananci, da yaren Rasha, da Larabci da yaren Sifaniya, da na Portuguese da kuma Faransanci.

Mashirya bikin sun ce masu aikin sa kan za su tallafawa masu halartar bikin baje kolin a fannin fassara, tun daga zuwansu har lokacin komawarsu kasashensu. Bikin dai zai gudana ne a tsawon mako guda, tun daga 5 ga watan Nowambar dake tafe a birnin Shanghai.

Kawo yanzu, sama da kasashe da yankuna 130 ne suka tabbatar da aniyarsu ta halartar wannan biki, wanda zai dada jaddada manufar kasar Sin ta gudanar da gyare gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda sauran sassan duniya za su samu karin damammaki na shiga kasuwannin kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China