in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka na bukatar damawa da mata a fannin shugabanci
2017-12-11 10:00:27 cri

Mataimakiyar daratan hukumar samarwa matasa aikin yi ta kasar Ghana Lydia Atiemo, ta ce akwai bukatar ba mata dama a bangaren shugabancin kasashe na nahiyar Afirka, muddun ana son samun ci gaba.

Da take ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua bayan kammala taron wakilan mata na Tarayyar Afrika da ya gudana a birnin Accran kasar Ghana, inda ta yi jawabi ga wakilai mata daga kasashen Afrika 50, Lydia Atiemo ta yi tsokaci sosai kan bukatar da Afrika ke da ita ta damawa da mata a siyasar kasashe da ma nahiyar.

Da take jadadda matakan da Ghana ta dauka ciki har da matakin samar da wata kafa da za a rika damawa da mata a dukkan matakan gwamnati, ta kuma bukaci mata su saita kansu, ta yadda za su ci gajiyar damarmakin.

A nata bangaren, daraktar cibiyar masana kan harkokin da suka shafi matasa ta kasar Afrika ta kudu Tessa Dooms, ta bukaci mata su daina dauka cewa sai wani ya tsaya musu a harkar siyasa.

Ita kuwa daraktar sadarwa ta shugaban kasar Ghana Fatimatu Abubakar gargadi ta yi ga mata game da mu'amala da bara gurbin 'yan siyasa.

Fatimatu Abubakar ta kuma bayyana gamsuwa game da yadda mata a Ghana ke da damar yin abun da suke muradi a fannin siyasa, duk da cewa har yanzu suna baya-baya da amfana da damar tsayawa takara musammam na majalisar dokoki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China