Peng Liyuan ta aike da sakon fatan alkhairi ga wadanda suka samu kyautukan a bana, wadanda suka hada da Gidauniyar Misr El Kheir ta Masar da kuma Gidauniyar Mata ta Jamaica.
A cikin sakon nata, ta ce ilimin mata da 'yan mata babban jigo ne wajen karfafa musu samun damarmakin cimma nasara a harkokinsu kamar takwarorinsu maza. Haka zalika ta ce muhimmiyar hanya ce, kana wani bangare ne na cimma muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ake son cimmawa ya zuwa 2030.
Har ila yau, ta ce kyautar hukumar UNESCO ga masu fafutukar ilimin mata da 'yan mata, ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafawa karin mutane gwiwar dukufa ga aikin. (Fa'iza Mustapha)