in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta gudanar da bikin ranar mata yayin da ake tsaka da kiran ba su kariya
2018-08-10 09:24:58 cri

Afrika ta Kudu ta yi bikin ranar mata ta kasar a jiya Alhamis, a daidai lokacin da ake tsaka da kiraye-kirayen kare mata daga cin zarafi.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya shaidawa mata mahalarta taron da ya gudana a yankin Mbekweni na birnin Paarl cewa, Afrika ta Kudu za ta samar da al'ummar da mata 'yan kasar za su yi rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali da kuma tsaro, yana mai cewa, dole a kawo karshen cin zarafi da gallazawa mata.

Ya ce, ya kamata mata su rika jin cewa akwai tsaro ko da suna kan titi ko a makaranta ko a wajen aiki.

A nata jawabin, Siyabulela Jentile, wadda ta assasa gidauniyar "Not in my Name" mai fafutukar tabbatar da daidaiton jinsi, ta kalubalanci maza su dauki mataki game da abubuwan da takwarorinsu ke aikatawa

Mata daga bangarori da dama na kasar ne suka yi tattaki a makon da ya gabata a Pretoria, domin nuna adawa da cin zarafin mata da musgunawa yara, inda kuma suka mika wasu jerin bukatu ga shugaba Ramaphosa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China