Niyi Ojuolape, wakilin UNFPA a Ghana, ya bayyana cewa, illolin dake tattare da wannan dabi'a yana hana mata da 'yan mata yancin jin dadin rayuwarsu da kuma hana su samun damammakin da suka dace, inda ya bukaci masu kishin al'umma a kasar Ghana da su tsaya tsayin daka don yakar wannan muguwar dabi'a.
Shi dai kaciyar mata ana yanke wani sashe ne daga al'aurar mace a matsayin al'ada ko kuma wasu dalilai da ba su shafi na kiwon lafiya ba.
Ghana tana daga cikin kasashe 29 na Afrika da yankin gabas ta tsakiya, inda ake fama da wannan al'ada, duk kuwa da kokarin da ake yi na neman kawo karshen dabi'ar kaciyar matan.
Ojuolape, wanda kungiyarsa ke fafutukar yaki da dabi'ar kaciyar mata, ya bayyana cewa, binciken kimiyya ya gano cewa wannan dabi'a tana da matukar illa kuma bai dace a cigaba da gudanar da ita a wannan zamani ba. (Ahmad)