Cikin wata sanarwa da ya fitar domin ranar 'yan mata ta duniya a jiya, Antonio Guterres, ya ce akwai abubuwa da dama da ke musu tarnaki, kamar nuna musu bambamci da rashin ba su horo, wadanda ke hana 'yan mata na wannan zamanin cimma nasarar a harkokinsu na rayuwa.
Ya ce galibi, 'yan matan ba sa samun damarmakin da suke bukata na kai wa ga ci, ya na mai cewa 'yan mata miliyan 600 ne ke shirin fara aiki a bangarorin kirkire-kirkire da kere keren kayakin fasahohi, wanda adadin matan da suka kammla karatu da wadanda ke aiki a wannan bangaren ba shi da yawa.
Antonio Guteress ya kara da cewa, adadin matan da suka kammala karatu a fannin fasahar sadarwa bai kai kaso 30 cikin 100 ba, haka kuma adadinsu a fannin ayyukan bincike bai kai kaso 30 ba a duniya. (Fa'iza Mustapha)