in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha za ta saukaka ka'idojin visa ga matafiya 'yan Afrika
2018-10-09 11:20:25 cri
Shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome ya ce nan gaba kadan kasarsa za ta baiwa 'yan kasashen Afrika damar shiga kasar ba tare da samun takardun izini na visa ba.

Teshome ya fadawa taron hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar cewa ana shirye shiryen aiwatar da tsarin bada takardun izinin visa ga matafiya daga kasashen Afrika da zarar sun sauka a kasar wanda dokar ta fara aiki tun a ranar 1 ga watan Satumbar wannan shekara.

Shuagabn kasar ya jaddada cewa Habasha, wadda ta sha karbar bakuncin tarurrukan kasa da kasa da na kungiyoyin shiyya kamar kungiyar tarayyar Afrika (AU) da hukumar MDD mai kula da kasashen Afrika, kasar tana daukar kwararan matakai don baiwa takwarorintsa 'yan kasashen Afrika damar shiga kasar ba tare da takardun visa ba.

Manufofin kungiyar AU na fafutukar samar da tsarin bai daya a tsakanin kasashen Afrika ya nemi a aiwatar da tsarin zirga zirga a tsakanin kasashen ta hanyar bada visa yayin da aka shiga kasar kafin nan da shekarar 2023.

Teshome ya ce, a matsayin Habasa na kasar dake da ofishin kungiyar tarayyar Afrika za ta aiwatar da wannan yarejejeniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China