An katse hanyoyin sadarwa na layukan waya da shafukan intanet saboda rudanin da aka shiga a babban birnin kasar.
Firaiministan kasar Abiy Ahmed ya gana da sojojin dake zanga zangar domin sauraron korafe korafensu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta tabbatar da hakan a jiya Laraba.
Zeynu Jemal, shugaban hukumar 'yan sandan kasar Habasha, ya shedawa 'yan jaridu cewa, zanga zangar da sojojin da suka gudanar wanda yawansu ya kai 240 ya haifar da katsewar al'amurra tare da sauran jami'an tsaro dake kusa da fadar gwamnatin kasar.
Da farko dai sojojin masu bore sun bukaci ganin firaiministan kasar ne a yayin da suke dauke da makamai, sai dai daga bisani bayan wata yarjejeniya, an ba su damar ganawa da Ahmed ba tare da makamansu ba, in ji Jemal.
Sojojin Habasha, suna daya daga cikin sojoji mafiya karfi da kuma yawa a nahiyar Afrika, an yabe su da halin nuna da'a, kuma ba kasafai aka fiya jin labarin boren sojojin na kasar ta yammacin Afrika ba, musamman a 'yan shekarun nan. (Ahmad Fagam)