in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan Habasha ya ce boren da sojojin kasar suka yi a kwanan nan ya saba dokar kasa
2018-10-19 10:25:03 cri
Firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya yi Allah wadai da boren da sojojin kasar suka yi a kwanakin baya inda ya bayyana matakin da cewa ya saba dokokin kundin tsarin mulkin kasar wanda hakan zai iya mayar da hannun agogo baya a yunkurin da ake na kawo sauye sauye a kasar.

A makon jiya ne wasu dakarun sojojin kasar Habasha su 250 suka yi gangami don yin zanga zanga a babban birnin kasar Addis Ababa, saboda abin da suka kira karancin albashi da rashin biyansu hakkokinsu, inda suka toshe hanyar zuwa gidan gwamnati da ofishin firaiministan kasar na dan wani lokaci.

Zanga zangar sojojin ta haifar da yin fito na fito a tsakaanin dakarun sojojin da jami'an tsaron ofishin firaiministan kasar, kasancewar sojojin sun bukaci ganawa da Ahmed.

Abey Ahmed, a lokacin da yake amsa tambayoyin mambobin majalisar wakilan kasar Habashan a jiya Alhamis, ya nanata cewa, boren sojojin ya saba dokokin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bayyana shi da cewa an gudanar da shi ne da wata boyayyar manufa domin lalata sauye sauyen da ake kokarin kawowa a kasar, da wargaza nasarorin da aka cimma karkashin sabbin manufofin gwamnatin kasar.

Firaiministan na Habasha ya ce, babu wani abu da masu kitsa wannan makarkashiya suke buri illa cimma wata boyayyar manufa, Ahmed ya tabbatar da cewa, ba don gwamnatinsa ta dauki matakan da suka dace ba wajen dakile boren sojojin, da an sake fuskantar tabarbarewar rikicin siyasa a kasar.

Ma'aikatar tsaron kasar Habasha ta sanar a wannan makon cewa, ta kama wasu mutane da ake zargin su ne suka kitsa boren sojojin.

Daga cikin wadanda aka damke a cewar sanarwar har da wasu manyan jami'an sojojin kasar, kamar yadda babban hafsan sojojin Habashan Seare Mekonnen, ya tabbatar da hakan.

Haka zalika, a jiya Alhamis Ahmed ya gargadi masu yunkurin ruruta wutar rikici a kasar wanda ke haifar da hasarar rayuka da dukiyoyin al'umma, da fashi da makamai, da su kula da kansu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China