Mulatu Teshome, ya bayyana haka ne yayin da ake tsaka da fama da karuwar rikicin kabilanci dake barazana ga sabbin ci gaban da aka samu a kasar dake gabashin Afrika.
A makon da ya gabata ne, ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, ya ce sama da mutane 70,000 sun tserewa gidajensu saboda rikicin kabilanci a jihar Benishangul Gumuz dake yammacin kasar.
Hare-hare a karshen watan Satumba ma sun tilatsawa mutane 15,000 tserewa matsugunansu tare da neman mafaka a makarantu da sauran gine-ginen gwamnati a fadin birnin Addis Ababa.
Shugaba Mulatu Teshome, ya yi kira ga al'ummar Habasha da su gujewa dabi'in da ka iya illata kasar. (Fa'iza Msutapha)