Wata takarda da kwamitin koli na JKS da majalisar gudanawar kasar suka fitar a Larabar nan, ta bayyana cewa, shirin zai mayar da hanlali kan masana'antu da wuraren da ba ta gari ke amfani da su wajen aikata munanan laifuffuka wadanda ke zama barazana ga tsaron jama'a.
Takardar ta ce, tsaron jama'a shi ne kashin bayan tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta yadda gwamnati za ta samu goyon bayan jama'a a matakin yankunan karkara. (Ibrahim Yaya)