Wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu kwafin ta a birnin Lagos, ta rawaito ministan watsa labarai da raya al'adu na kasar Lai Mohammed, na ce gwamnatin kasar ta kadu matuka, da samun labarin kisan jami'ar ta Red Cross, duk kuwa da matakan da gwamnati ta dauka na kaucewa hakan, da ma kiraye kiraye da aka yi ta yi daga sassa daban daban, na ganin matashiyar ta tsira da ranta. (Saminu Hassan)