in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria da Nijeriya za su bunkasa manyan ayyukan da suke gudanarwa
2018-10-16 09:50:19 cri
Kasashen Algeria da Nijeriya, sun rattaba hannu kan shirin bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki a tsakaninsu, a lokacin da Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ke ziyara a birnin Algiers.

Yarjejniyar da Ministan harkokin wajen Algeria Abdelkader Messahel da takwaransa na Nijeriya suka sanyawa hannu yayin taron kwamitin hadin gwiwa ta kasashen biyu, ta ce hadin gwiwar ta shafi bangarorin samar da makamashi da sufuri da sadarwa.

Abdelkader Messahel, ya ce yarjejeniyar ta yi bayanin matakai daban-daban na aiwatar da kudurorin bangarorin biyu.

Ya kuma jinjinawa manyan ayyukan da kasashen biyu suka kaddamar, da ya hada da babbar titin dake hada birnin Algiers da Lagos na Nijeriya, da kuma wayar sadarwa ta karkashin kasa da ta hada manyan biranen kasashen biyu da kuma bututun iskar gas da ya hada su, wanda kuma zai ba Nijeriya damar tura gas zuwa Turai, ta bututun da ya ratsa Niger da Algeria.

A nasa bangaren, Geofferey Onyeama ya ce Nijeriya na da burin karfafa dangantakarta da Algeria, ya na mai cewa sun je Aljeria ne domin bunkasa dangantakar dake tsakaninsu da kuma kara kaimi ga ayyukan da bangarorin biyu suka kaddamar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China