Xi Jinping ya nuna cewa, yin cudanya da koyi da juna kan al'adu, muhimmin karfi ne wajen ciyar da bunkasuwar wayewar kan al'umma da zaman lafiyar duniya gaba. Kullum dan Adam na samun ci gaba ne a yayin da ake mu'ammala tsakanin kabilu da al'adu iri daban daban.
Baya ga haka, Xi ya jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa kan kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa mai adalci irin ta girmama juna, da neman hadin kai da samun nasara tare, ya kuma yi kira ga kasashe daban daban don su yi kokari tare wajen kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Bilkisu)