"A halin yanzu hukumar tana fama da manyan kalubaloli na karancin kudade wanda yana bukatar dukkan bangarorin da abin ya shafa su sa kai wajen sauke nauyin dake wuyansu ta hanyar bada gudumawarsu," in ji Ma Zhaoxu zaunannen wakilin Sin a MDD yayin da ya bayyana hakan a taron kwamitin gudanar da kasafin kudi na MDD karo 5 a ranar Talata.
Ma ya ce, akwai kura kurai da ake tafkawa wajen yadda ake tantance kason kudaden da kowace kasa za ta bayar bisa la'akari da banbancin dake tsakanin kasashen da suka ci gaba da kasashe masu tasowa..
Game da batun kiyasin ayyukan wanzar da zaman lafiya kuwa, kasar Sin tana goyon bayan a gudanar da ayyukan hadin gwiwa da daukar nauyi ayyuka na musamman, in ji jakadan na Sin.
Duk da bunkasuwar tattalin arzikin da take samu, "kasar Sin har yanzu kasa ce mai tasowa idan aka yi la'akari da ma'aunin kudaden shigar jama'ar kasar wanda yake a matsayi na 70 a duniya," jakadan ya nanata cewa, kasar Sin za ta kara tallafinta wajen shirin wanzar da zaman lafiya nan MDD daga shekarar 2019-2021. (Ahmad Fagam)