in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda suka mutu a fashewar bututun mai a Najeriya sun kai 60
2018-10-16 09:14:40 cri
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta sanar a jiya Litinin cewa, mutanen da suka mutu a sanadiyyar fashewar bututun mai a jihar Abia dake kudancin Najeriya sun kai 60.

NEMA ta bada sanarwar ne bayan tattara alkaluman adadin wadanda lamarin ya rutsa dasu a karamar hukumar Osisioma ta jihar Abia a ranar 12 ga watan Oktoba.

Evans Ugoh, jami'in hukumar bada agajin gaggawa na jahohin Abia da makwabciyarta jihar Imo, ya ce sakamakon binciken farko ya nuna cewa rashin kulawa da yanayin da bututun man ke ciki ne ya haddasa matsalar.

Bututan mai, mallakar kamfanin mai na Najeriya, an yi watsi dasu ba tare da duba halin da suke ciki ba a tsawon lokaci, hakan ne ya haddasa suke yoyo, inji Ugoh.

Jami'in ya zargin wadanda hadarin ya rutsa dasu da laifin kin sanar da hukumomin da abin ya shafa game da yoyon da bututan man ke yi.

Wadanda lamarin ya rutsa dasu, galibinsu mazauna yankunan Umuimo da Umuaduru ne a jahar ta Abia, inda suka yi gangancin kwasar man a lokacin da bututan man suka fara yoyo, in ji shi. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China