in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya sabunta matakan yaki da safarar bakin haure daga Libya
2018-10-04 15:54:47 cri
A jiya Laraba kwamitin tsaron MDD ya amince da sabunta dokokin binciken manyan jiragen ruwa tare da kwace jiragen daga gabar tekun Libya a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure da safarar bil adama.

Kudurin kwamitin MDDr mai lamba 2437, wanda ya samu amincewar dukkan kasashe mambobin kwamitin MDDr 15, ya amince da sabunta wa'adin watanni 12 tun daga ranar da aka amince da kudirin.

Kudirin ya baiwa kasashe mambobin kwamitin dama su gudanar da ayyukansu a matakai na kasashen ko kuma ta hanayar kungiyoyi na shiyyoyi, domin bincika manyan jiragen ruwa wadanda ake zargin ana amfani da su wajen yin fasa-kwauri ko kuma safarar bil adama daga Libya. Kudirin ya ba da damar kwace jiragen ruwa wadanda aka tabbatar da cewa ana amfani da su wajen gudanar da wadannan ayyuka.

Tun bayan kifar da gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasar Libya a shekarar 2011, gabar tekun kasar ta kasance a matsayin wata matattarar da ake amfani da ita wajen safarar bil adama da kwararar bakin haure. Mafi yawan bakin hauren dake Libyan sun fito ne daga kasashen yankin hamadar Saharar Afrika a kokarinsu na tsallakawa kasashen Turai. Mafi yawan bakin hauren suna karewa ne a matsayin bayi wadanda ake fataucinsu a Libya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China