Babban jami'in 'yan sandan jahar Abia Anthony Ogbizi, ya ce an sake samun karin mutane 5 da suka mutu wadanda da farko sun tsira da munanan raunukan konar wuta bayan da aka samu fashewar bututun mai a kauyuka biyu dake jahar a ranar Juma'a.
Ogbizi ya dora alhakin fashewar da yoyon da bututun mai ke yi a sakamakon aikin gyaransu da ake gudanarwa a halin yanzu, sai dai ya ce, ana ci gaba da gudanar da karin bincike kan lamarin.
A ranar Juma'a, hukumar tsaron rayukan al'umma ta Civil Defense ta zargi wasu matasan yanki da laifin kwasar man fetur bayan fashewar bututun man.
A 'yan shekarun da suka gabata Najeriya ta sha fama da matsalar yawan fasa bututan mai. Mafi yawa tsagerun yankunan masu albarkatun mai ne ke lalatawa domin kwasar man. (Ahmad Fagam)