Sanarwar da hukumar IOM ta fitar, ta ce sama da bakin haure 500 ne suka karbi kayakin agaji da aka raba, sun hada da katifu da barguna da kayakin tsafta a cibiyar Shuhada Al Nasr, sai dai kuma hukumar ta ce bukatun bakin hauren ya zarce wadannan.
Har ila yau, hukumar ta yi alkawarin ci gaba da samar da kayakin bukata ga bakin hauren hauren dake akwai.
Cibiyoyin dake karbar bakin haure a Libya na cike makil da mutanen da aka tsare ko wadanda hukumomin kasar suka ceto daga tekun Bahr Rum. (Fa'iza Mustapha)