A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aikawa Barham Salih sakon taya murnar zama shugaban kasar Iraki.
A cikin sakon nasa shugaba Xi ya bayyana cewa, yana farin cikin ganin yadda a 'yan shekarun nan dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Iraki ke ci gaba da wanzuwa, matakin da ya taimaka wajen karfafa aminci a tsakaninsu da bunkasa alakar musaya tsakanin al'ummominsu.
Xi ya kuma bayyana fatan cewa kasar Iraki za ta samu ci gaban sasantawa a fannonin siyasa da sake gina tattalin arzikin kasar, za kuma ta yi kokarin samun hanyar raya kasar da ta dace da kasar karkashin jagorancin Salih
A ranar 2 ga watan Oktoba ne majalisar dokokin kasar Iraki ta zabi Salih a matsayin sabon shugaban kasar.(Ibrahim)