Xi, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin halartar taron kwamitin tsakiya mai kula al'amurran kudi da tattalin arziki.
"A matsayin wata babbar hanyar samar da kariya daga afkuwar bala'u daga idallahi wanda zai iya shafar tattalin arziki da rayuwar jama'a, kasar Sin za ta kafa wani ingantaccen tsarin kimiyya da kuma inganta yanayin al'umma ta yadda za'a samu damar bada kariya ga rayuwar al'ummarmu da dukiyoyinsu da kuma tabbatar da tsaron kasa," Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a gun taron.
Xi ya kuma yi tsokaci game da aikin gina layin dogo daga yankin Sichuan zuwa Tibet, yana mai cewa, wannan mataki ya nuna muhimmancin manufofin da kasar ta Sin ta jima tana tsarawa don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin Tibet. (Ahmad Fagam)